Yadda aka yi husufin rana a ƙasashen duniya

0
481

Ɗimbin jama’a sun shaida kisfewar rana a wani bangare na Yammacin Afrika da Kasashen Larabawa da India da kuma yankin Gabashin Duniya mai nisa.

Ana samun husufin rana ne a lokacin da wata ya ratsa tsakanin doran kasa da kuma rana, lamarin da ke hana duniya samun isasshen hasken rana, inda ake iya hangen kurin rana mararan a can sararin samaniya.

Kisfewar ranar na aukuwa ne a duk shekara ko kuma shekaru biyu-biyu, kuma wani bangare na al’ummar duniya ne ke shaida lamarin.

An fara hangar kisfewar ta ranar Lahadi a yankin arewa maso gabashin Jamhuriyar Congo daga karfe 5 da minti 56 na safe agogon kasar, wato jim kadan da bullowar rana, inda aka dauki tsawon minti 1 da dakika 22 na kisfewar.

Daga nan kisfewar ta doshi wasu sassan Afrika da Asiya, inda a yankin Uttarakhand na India, kusa da kan iyakar kasar da China, jama’a suka shaida yadda kaskon rana ya dishe sosai da misalin karfe 12 da minti 10,.

A can birnin Nairobi na Kenya da ke gabashin Afrika kuwa, ‘yan kallo sun hangi wani bangare ne na dishewar rana, lura da cewa, an samu girgije da ya mamaye sararin samaniya na tsawon dakioki.

Yanzu haka dai masana yanayi sun yi hasashen cewa, a ranar 5 ga watan Yuli mai zuwa, za a samu kisfewar wata, kuma a cewarsu, za a fi jin dadin kallon kisfewar a Arewaci da Kudancin Amurka da yankin Kudancin Kasashen Turai da kuma nah iyar Afrika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here