Yadda Aminu Gadanya ya zama samu nasarar lashe zaɓen ƙungiyar lauyoyi ta Kano

0
101444

Ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen jihar Kano wato NBA ta zabi Aminu S Gadanya a matsayin sabon shugabanta.

Tun da farko shugaban kwamitin gudanar da zaben Tajuddeen Funsho ne ya sanar da sakamakon zaɓen, inda Aminu S Gadanya ya samu ƙuri’u 214 inda ya yi nasara akan Aminu Garba Waru, wanda ya samu ƙuri’u 137, sai kuma Usman Umar Fari da ya samu ƙuri’u 38.

Sauran muƙaman da aka zaɓa sun haɗa da Isma’il Abdulazeez a matsayin ma’ajin ƙungiya da kuma Mukhtar Shehu Bello a matsayin mataimakin sakatare, sai kuma Asma’u Muhammad a matsayin sakatariyar walw ala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here