29.2 C
Nigeria
Monday, September 27, 2021

Yadda Buhari, El-Rufai da Yahaya Bello su ka jefa ƴan Najeriya a cikin ruɗani a cikin kwanaki 3

Must read

A daidai lokacin da talauci a Najeriya ke ƙara karuwa, mutane na tsananin jin jiki. Abinci tsada, kayan masarufi tsada, tsadar rayuwa, komai tsada.

Hakazalika kuma al’umma na matukar kokawa da yanayin matsin rayuwa da ake fama da shi, musamman na karancin kudaden biyan bukatu na yau da kullum a hannunsu.

Sai katsam wasu rahotanni su ka rawaito cewa hukumar haraji ta jihar Kaduna ta sanar da dawo da karɓar wannan haraji, wadda ta ce wajibi ne ga duk wanda ya haura shekara 18 ya riƙa biyan naira 1,000 duk shekara a matsayin haraji.

Masu sharhi da al’ummar a jihar Kadunan sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da sabon harajin naira 1000 kan kowane baligi a kowace shekara, da hukumar tattara harajin jihar za ta fara aiwatarwa a sabuwar shekara mai kamawa.

Dawo da wannan doka ta biyan harajin naira 1,000 da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa’i ya yi a wannan lokaci, ta haɗu da tsaiko tare da shan suka daga mutane daban-daban, musamman la’akari da cewa hukumomi a jihar ta Kaduna ba su wayar da kan al’ummar muhimmancin haraji yadda ya kamata ba.

A daya ɓangaren kuma akwai rashin yadda tsakanin talaka da hukuma. Domin mafi yawan talakawan Najeriya ba su yadda da amanar dukiyarsu a hannun shugabanninsa ba. Da yawa kallon su ake a matsayin barayi kawai, ƴan ta more da su ka yi rub da ciki akan dukiyarsu.

Al’ummar Najeriya musamman a shafukan Intanet ba su kai ga kammala yin sharhi tare da taya mutanen Kaduna su ka samu kan su ba, sai kawai aka ji yo amon gwamnatin jihar Kogi na fito da wani sabon tsari na biyan haraji ga kowanne sunƙin biredi a jihar.

Ma’aikatar kasuwanci da masana’antu ta jihar ta ce wannan harajin zai taimaka wurin samun kuɗin shiga a jihar ta Kogi.

Jama’a a Najeriya da dama sun kalli wannan abu tamkar almara, domin gwamnan jihar Yahaya Bello, yana wa’adin zangon mulkinsa na biyu amma babu wani abin a zo a gani a jihar da za a ce gwamnatinsa ta yi, domin har wasu suna jallon gwara jiya da yau.

Haka kuma masu sharhi akan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa idan har sauran harajin da ake karɓa a jihar bai bunƙasa abin da jihar ke samu daga haraji ba, to harajin biredin da ake ƙoƙarin ƙirƙirowa babu abin da zai yi face ƙara jefa talakawan jihar a cikin halin ƙunchi.

A cikin kwana na uku kuma sai kawai ƴan Najeriya su ka wayi gari da sanarwar hukumar ƙayyade farashin man fetur ta Najeriya wato PPMC ta ƙara kuɗin man fetur a depo-depo zuwa 155.17, Allah Sarki Makam Talaka.

Shugaban ƙungiyar manyan dillalan man fetur na arewa maso yamma, Bashir Ɗanmalam ya bayyana cewa gidajen mai za su fara sayar da man fetur tsakanin naira 168 zuwa naira 170, saɓannin naira 158 zuwa naira 160 da ake sayarwa a baya.

Labarin ƙarin farashin man fetur ya zo wa ƴan Najeriya cikin bazata, ganin yadda ake zaman ƙuncin taɓarɓarewar al’amurra dalilin barkewar cutar Korona.

Tabbas a cikin kwanaki uku shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da takwaransa na jihar Kogi Yahaya Bello sun jefa talakawan Najeriya cikin ruɗani da kuma taraddadi.

 

 

 

 

 

- Advertisement -spot_img

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -spot_img

Latest article