Yadda Godswill Akpabio ya tunawa wasu ƴan majalisu asiri a kan kwangila

0
3390

Ministan Raya Yankin Niger Delta, Godswill Akpabio ya bayyana sunayen ‘yan majalisun da Hukumar NDDC ta bai wa kwangilar gudanar da wasu manyan ayyuka. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin shugabannin Hukumar Raya Yankin na Niger Delta NDDC da handame makuden kudade.

Daga cikin sunayen ‘yan majalisun da suka karbi kwangilar har da shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai Kula da Yankin Niger Delta, Peter Nwabaoshi wanda ya karbi jerin kwangiloli har guda 53 kamar yadda Minista Akpabio ya sanar.

Mista Akpabio ya kuma ce, Sanata Mathew Urhoghide ya kabi kwangiloli shida, sai Sanata James Manager da shi ma ya karbi kwangiloli shida, yayin da tsohon Sanata, Samuel Anyanwu ya karbi 19.

Kazalika tsohon shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da Hukumar NDDC, Nicholas Mutu, ya amshi kwangiloli har guda 74, wanda shi ne adadi mafi girma kamar yadda Akpabio ya bayyana a cikin wasu takardu da ya aike wa kwamitin da ke gudanar da bincike kan zargin almundahana a Hukumar Raya Yankin Niger Delta.

Har ila yau an samu wasu ‘yan tsirarun ‘yan majalisu daga Ondo da Edo da suka karbi kwangilolin daga hukumar ta NDDC.

Takardun da Akpabio din ya fitar, sun nuna cewa, an bada akasarin kwangilolin ne a shekarar 2018, amma ba a bayyana adadin kudaden da aka kashe ba wajen gudanar da su.

Wannan na zuwa ne bayan kakakin Majalisar Wakilai na ƙasa Femi Gbajabiamila ya yi barazanar maka Akpabio a kotu bisa zargin sa da yunkurin bata wa ‘yan majalisun suna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here