Yadda Gwamnan Zulum ya tsallake rijiya da baya daga harin ƴan boko haram

0
2938

Gwanman jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tsallake rijiya da baya a wani harin kwanton Bauna da mayakan Boko Haram su ka kai masa a Arewacin jihar Borno.

Rahotanni da wadan da ke cikin tawagar sa su ka bayar sun tabbatar da cewa Gwamna Zulum ya tsira daga harin ba tare da wani abu ya same shi ba.

Yanzu haka dai tawagar Gwanan ta isa Munguno domin ci gaba da ziyarar aiki da ya ke yi.

Gwamnatin shugaba Muhammadu, Buhari dai ta dade tana ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin arewa maso gabashin kasar nan, amma har yanzu mayakan kungiyar na ci gaba da yi wa mutanen yankin barazana.

Mayakan na Boko Haram dai sun kwashe fiye da shekara goma suna kai hare-hare a arewacin Najeriya, musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here