Yadda jami’o’in Najeriya su ka duƙufa kan binciken samar da maganin cutar korona

0
4554

Yanzu haka wasu cibiyoyin bincike a Najeriya na kan hanyar samar da maganin rigakafin cutar COVID-19 wadda ta addabi kasashen duniya ta kuma lakume rayukan mutane kusan 700,000.

Shugaban Hukumar kula da Jami’oin ƙasar nan, Farfesa Abubakar Rasheed ya sanar da wannan cigaban da ake samu a Jami’ar Redemeer dake hada kai da Jami’ar Cambridge, tare da wasu Jami’oi guda 6 da suka hada da Jami’ar Jos da Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria da Jami’ar Lagos da Jami’ar Obafemi Awolowo da Jami’ar Olabisi Onabanjo da kuma Jami’ar Igbinedon.

Farfesa Rasheed yace binciken da wadannan cibiyoyi ke gudanarwa ya shafi magungunan gargajiya da ake yiwa gwajin kimiya domin ganin tasirin su kan cutar domin gano maganin da ake bukata.

Shugaban Hukumar ya ce Jami’ar Redeemer ce gaba wajen zama cibiyar gwaji da tantance maganin kafin daga bisani Jami’oin Ahmadu Bello da bayero da lagos da Jos da wasu kuma suka shiga ya zuwa ranar 22 ga watan Yunin wanna shekara, kuma yanzu haka jami’oi 32 a Najeriya ke gudanarwar da irin wannan bincike daban daban.

Farfesa Rasheed ya ce bayan bincike akan maganin rigakafin, Jami’oi da dama sun gudanar da wasu bincike daban daban da suka hada da samar da na;urar taimakawa marasa lafiya yin numfashi da na’urar rufe fuska da wasu kayayyakin kula da lafiyar a l’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here