Yadda mutane 43 su ka rasa ransu sakamakon zaftarewar ƙasa a India

0
2986

A kalla gawarwakin mutane 43 aka gano a kasar India, bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ta haifar da mummunar ambaliya ta kuma zaizayar kasa, wanda ta mamaye gonakin shayi a kudu maso yammacin Indiya.

Shugaban ‘yan sandan gundumar Idukki, yankin na lamarin ya auku, Karuppasamy, yace lamarin ya wakana ne tun ranar jumma’a, kuma akasari wadanda iftil’an ya riska ma’aikatan gonan shayin ne.

A daren jumma’a dai gawawwakin mutane 18 a ka gano, kafin adadin ya karu zuwa 43 da maraicen yau Lahadi, sai dai wasu Kafofin yada labaran Yankin sun ce mutane 78 suka bata.

Mutane sama da 300 suka mutu sakamakon ambaliya da zabtarewar kasa a gabashi da arewa maso gabashin India a makowannin da suka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here