Yadda wani Limami ya ɗaure ɗansa a gida tsawon shekaru 15 a Kano

0
3047

Rundunar ƴan sanda ta ƙasa reshen jihar Kano ta kai samame gidan limamin Juma’a na unguwar Fulani dake Sheka a ƙaramar hukumar Kumbotso.

Rahotonni sun bayyana cewa a yayin samamen ƴan sanda sun gano ɗan limamin mai suna Ibrahim Lawal da ake zargin mahaifinsa ya kulle shi har tsawon shekaru sha biyar.

Wata majiya mai tushe ta shaida mana cewa, ‘yan sanda basu samu limamin a gida ba, inda rahotonni suka ce limamin ya tafi ƙauye sai matarsa kaɗai ƴan sanda suka iske.

Har zuwa wannan lokaci dai rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ba ta yi ƙarin haske a kan lamarin ba.

Ko a watan Satumba na shekarar 2019 wasu rahotanni sun bayyana yadda wani mutum mai suna Muhammadu Ojudi dake garin Rinji a ƙaramar hukumar Madobi, ya kulle ƴaƴansa biyu da sarƙa har tsawon wasu shekaru.

A ƙarshe Muhammadu Ojudi ya rasa ransa yayin da hukumomi ke dab da fara bincikarsa, daga bisani kuma jami’an lafiya a Kano suka tabbatar da cewa, ƴar sa guda ɗaya daga cikin waɗanda ya kulle ta samu taɓin hankali sanadiyyar wannan ɗauri.

Haka ma a ranar Larabar da ta gabata ƴan sanda sun ceto wani matashi a unguwar Farawa wanda mahaifinsa ya kulle shi tsawon shekaru bakwai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here