YAJIN AIKI: Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa Asibitoci 31 Sama Da Naira Biliyan Hudu

0
184

Gwamnatin tarayya ta saki kudi har naira biliyan 4.5 ga asibitocin koyarwa na gwamnatin tarayya guda 31 a fadin kasarnan, inda kuma ta ayyana naira biliyan 9 domin biyan kudin inshorar lafiya.

Dr Chris Ngige, ministan kwadago shi ne ya bayyana hakan tare da ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, a yayin da suke yiwa manema labaran gidan gwamnati bayani bayan zaman sirri da suka gudanar tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Zaman ya gudana ne a fadar gwamnati dake Abuja.

Ngige ya ce sun ware naira biliyan 4.5 domin biyan kudaden alawus na watan Afrilu da kuma Mayu, sannan kuma za a biya na watan Yuni ba tare da bata lokaci ba. Ya ce za su biya kudin ne domin biyan bukatar kungiyar Likitocin Nijeriya, NARD wadanda suke yajin aiki a halin yanzu.

Ministan ya nuna karfin guiwarsa na cewa yajin aikin da kungiyar Likitocin Nijeriyar ke yi za su kawo karshensa tunda sun cika musu alkawuransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here