‘Yan Kasuwar Maradi Sun Bayyana Irin Ci Gaban Da Jami’ar MAAUN Ta Kawo Wa Jiharsu

0
58

Wasu matasa ‘yan kasuwa a Maradi dake Jamhuriyar kasar Nijar, sun yaba wa mamallakin Jami’ar Maryam Abacha (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo saboda kawo ci gaba da bunkasa tattalin arzikin jihar Maradi da ma Jamhuriyyar Nijar baki daya ta hanyar kafa wannan Jami’ar.

Daya daga cikin ‘yan kasuwar Maradi, Alhaji Abdulkadeer Sani Gwanda, ya yi wannan jawabin ne a wata liyafa ta musamman da’ yan kasuwar suka shirya don girmama Farfesa Gwarzo a Maradi, Jamhuriyar Nijar a ranar Asabar. Ya ce kafa Jami’ar Maryam Abacha a Maradi ba kawai ta kawo ci gaba bane, harma da bunkasa ayyukan zamantakewa da jama’ar jihar.

Ya kara da cewa; wannan dalilin yasa suka yanke shawarar girmama Farfesa Gwarzo sakamakon gudummawar da ya bayar wajen ci gaban tattalin arziki da ci gaban garin Maradi dama Jamhuriyar Nijar baki daya. Ya ce mutanen Maradi musamman ‘yan kasuwa za su ci gaba da godiya da irin gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban tattalin arziki da ci gaban garin.

Sani Gwanda wanda shi ne mai babban Plaza a Maradi, ya ce Farfesa Gwarzo ya cancanci a karrama shi ne saboda irin tallafin da yake bayarwa ga matasa da talakawa da sauran jama’a musamman na irin mawuyacin da wasu ke shiga a garin amma yana taimaka musu.

“Farfesa Gwarzo mutum ne mai kirki sosai, Duk goyon baya da taimakon da ya yi wa mutanenmu ba za mu taba mantawa dashi ba. Shi mutum ne na musamman wanda a shirye yake a ko da koyaushe don tallafawa matasa don inganta matsayin zamantakewarsu da tattalin arziki a cikin al’umma.”

Har wala yau a wani bangare na bayaninsa, ya kara da cewa; “Baki a jihar nan ba za su iya gaya muku ko wane ne Farfesa Gwarzo ba, amma mu da aka haifa mu ne zamu gaya muku wane ne shi. Ba za mu iya biyan shi ba, amma Allah madaukakin Sarki kaɗai zai iya biya shi abin da ya mana,” inji shi.

Da yake karin haske kan dalilansu na karrama Farfesa Adamu Gwarzo, sun karrama shi ne saboda irin gudummawar da yake bai wa jihar Maradi da tallafawa matasa da ‘yan kasuwa da ma kasar Jamhuriyar Nijar baki daya. Wanda ya ce hakan ya sanya ma suka gayyaci matasa da ma ‘yan kasuwa baki daya domin halartar wannan taro. “Kafa Jami’ar nan kawai da ya yi ci gaba ne gare mu, idan da ya so zai iya zuwa wani wuri ya yi ta a Nijar ma kadai. Amma ya zabi ya yi ta a wurinmu, wanda hakan ya kawo mana ci gaba sosai. Idan ka yi Jami’ar, kowa ya san yadda tattalin arziki yake bunkasa saboda yadda ‘yan makaranta ke zuwa da yawa, suna kuma cefane-cefane, daukar A Daidaita, biyan wuta, wannan ya kara bunkasa mana tattalin arzikinmu. Yana damuwa da Talakawa sosai. Yana samun ‘yan kasuwa yana bunkasa musu kasuwancinsu. Gari yana matukar amfana da abin da yake yi, ba za mu iya biyansa ba, sai dai kawai Allah ya biya shi.” Ya tabbatar.

A wani bangare na bayaninsa a yayin zantawa da Abdulkadeer Gwanda, ya kara da cewa; “Irin Farfesa Adamu Gwarzo ba a samunsu sosai irin wannan lokacin. Zamu ba shi dukkanin goyon baya da addu’o’i. Muna kira ga shugabanninmu da su taimakawa Farfesa Adamu Gwarzo. Wane irin taimako za a iya mishi? Domin ya samu ya ci gaba da taimakawa mutane da dalibai domin su samu su yi karatunsu cikin rufin asiri, cikin mutunci, mu shi kawai muke son su dafa mishi.” Inji shi.

Sannan ya yi kira ga ‘yan jihar Maradi da su ci gaba da ba shi hadin guiwa da goyon baya wanda hakan zai sanya kokarin da yake yi ya sake bunkasa sosan gaske a kafatanin jihar baki daya. “Domin mun ga bambancin zuwansa da kafin zuwansa garin nan.” ya lurantar.

A karshe ya yi kira ga gwamnati da jama’ar Jamhuriyar Nijar da su ci gaba da tallafa wa Farfesa Gwarzo da ba shi goyon baya domin ba shi damar cimma burin da yake so.

“Saboda haka Farfesa Gwarzo yana da jama’ar Maradi da zuciyarsu a hannunsa, saboda haka ko yanzu in yana so zai iya kafa Jami’a a wani wuri a fadin Jihar nan”. Ya Tabbbatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here