‘Yan Sanda Sun Garkame Jagoran Zanga-Zangar #ArewaIsBleeding

0
106

Rahotanni na nuni da cewa jami’an tsaron ‘yan sanda sun damke Nastura Ashir Sharif bisa shirya zanga-zangar lumana da ya gudanar a jihar Katsina kan yawaitar kashe-kashen da yake gudana a Arewacin Nijeriya.

A ranar Talata ne, Sharif, shugaban gamayyar kungiyoyin Arewa ta CNG, suka gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jindadinsu bisa yadda ‘yan bindiga ke kashe-kashe a yankin.

CNG,  a cikin wata sanarwa da suka wallafa a shafinsu na Facebook sun bayyana cewa, an tafi da Sharif birnin tarayya Abuja bayan kammala zanga-zangar.

Shugaban gamayyar kungiyar, a cewar CNG ana ci gaba da tsare shi ne a hedikwatar ‘yan sanda dake Abuja. “Sakamakon yana tir da kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba da ‘yan bindiga ke yi.” Inji sanarwar.

Wata majiya ta labarta Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Katsina ne ya tafi da Sharif daga Katsina zuwa Abuja, inda Kwamishinan ‘yan sandan ya shaidawa shugaban matasan cewa; sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya ne yake son ganinsa a Abuja, inda suka tafi tare.

“Bayan sun isa Abuja, sai suka garkame shi a hedikwatar ta su.” ya labarta.

A yayin zanga-zangar, masu zanga-zangar sun nemi shugaba Buhari da gwamna Masari da su sauka akan mukamansu bayan gaza kare rayukansu da suka kasa yi.

Sai dai da suke mayar da martani, fadar shugaban kasar sun ce; masu zanga-zangar su godewa Allah ya zama Nijeriya mulkin Dimokuradiyya ake yi. Kalamin da aka rika Allah-wadai da shi a kafafen sada zumunta.

Har wala yau a lokacin zanga-zangar, wani wanda ya shiga zanga-zangar wanda ya zo tun daga garin Faskari ta jihar Katsinar, ya labarta yadda aka kashe abokinsa a yayin da ‘yan bindigar suka nemi yi wa matarsa fyade ya ki yarda, ita ma matar ta ki yarda, inda ‘yan bindigar suka kashe su dukkansu.

Sai dai a na shi bayanin, gwamna Masari ya ce tabbas ya gaza kare rayukan  mutanen Katsina, inda ya nemi afuwarsu da gafararsu.

Ko kafin nan, sai da kungiyar CNG din ta caccaki gwamnatin na Buhari bisa martanin da gwamnatin ta mayarwa kungiyar Dattawan Arewa ta NEF bayan ta koka da kashe-kashen da ake yi a Arewa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here