Rundunar Yan Sandan kasarnan ta saki Nastura Ashir Sharif bayan ta tsare shi a ranar Talata sakamakon shirya zanga-zanga a jihar Katsina.
Nastura ya samu yanci ne a yammaci yau bayan ya shafe kwana daya a shelkwatar yan sandan da ke Abuja.
An dai shirya zanga-zangar ne sakamakon kashe-kashen rayuka da ake fama dashi a Arewacin kasarnan.