‘Yan Shi’a Aka Fi Danne Wa Hakki Fiye Da Kowa A Nijeriya, Inji Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama

0
5059

Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil’adama da wasu kungiyoyin fararen hula na Arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, sun bayyana cewa Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky sune mutanen da aka fi take wa hakkin cikin shekaru 40 da kafa Harkar fiye da kowanne mabiya a Nijeriya baki daya.

Gamayyar kungiyoyin sun bayyana hakan ne a yayin taron ‘yan jarida da suka kira a Otel din Bolingo dake birnin tarayya Abuja a yau Asabar 4 ga watan Yulin 2020 dangane da rashin tsaro da kuma take hakkin bil’adama a Nijeriya.

Kungiyar ta yi tilawar cewa daya daga cikin take hakkin da aka yi wa mabiya El-Zakzaky din ya hada da yadda rundunar sojan Nijeriya a karkashin jagorancin Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai suka yiwa mabiya El-Zakzaky din kisan kiyashi a cikin watan Disambar 2015; “Da sunan wai an tarewa Burutai hanya za a halaka shi, wanda hakan ya sanya sojojin suka kashe dubban marasa makami.” Inji kungiyar.

Gamayyar kungiyoyin sun nuna bacin ransu kan yadda rundunar sojin Nijeriya suka yiwa mabiya El-Zakzaky din kisan gilla; “tare da kona wasun su da ransu, yiwa wadansu fyade, rushe muhallansu, da kuma bizne daruruwansu a ramin bai daya. Tabbas ba za mu manta da wannan danyen aikin ba a ci gaba da fafutikar da muke yi wajen kare hakkin bil’adama a kasarnan.” Suka tabbatar.

Har wala yau a wani bangare na bayaninsu, sun bayyana cewa gwamnatin Nijeriya ta sabawa sashe na 33, 34, da kuma 36 na kundin tsarin mulkin 1999; “wanda ya ce kowanne dan Adam yana da ‘yancin rayuwa, kuma ba wanda za a hana ma wannan ‘yancin haka siddan. Kuma dole a hukunta wadanda aka samu wajen aikata wannan danyen aikin. Domin babu dan Nijeriya da ya dace a nuna wa wariya saboda abin da ya zabi ya yi, ko saboda kabilarsa, jinsinsa, muhallinsa, da kuma ra’ayin siyasarsa.” Suka lurantar.

Haka zalika kungiyar sun nuna yadda gwamnatin Nijeriya a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta nuna wa mabiya El-Zakzaky wariya da kiyayya. “Har wala yau an dakile musu ‘yancin bayyana ra’ayi akan kisan kiyashin Zariya idan aka yi duba da kwamitin binciken kisan kiyashin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa, da kwamitin da fadar shugaban kasa da ta kafa kan take hakkin bil’adama da rundunar sojin Nijeriya ta yi.” Inji su.

Gamayyar kungiyar ta ce; mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya, suna da ‘yancin gudanar da rayuwarsu da kuma mallakar wurare da ake ci gaba da rusa musu. “wanda a wani lokacin ma ake danne musu wannan hakki.”

A karshe gamayyar kungiyar sun yi kira ga gwamnatin Nijeriya da su bai wa kotun hukunta laifukan ta’addanci ta duniya, ICC hadin kai bisa laifukan da ake zargin Nijeriya da aikatawa da ya hada da na take hakkin ‘yancin bil’adama, tare da kamawa da kuma mika wa ICC dukkanin jami’an da suke da hannu wajen kisan kiyashin da aka yiwa ‘yan shi’a domin a yi musu hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here