Rundunar Yan Sandan kasarnan sun rufe babban ofishin jam’iyya mai mulki ta kasa, wato APC, a yau dinnan.
Babban Speton Yan Sanda na Kasa, IGP Muhammed Adamu ne ya bada umarnin rufe ofishin, inda akayi hakan don samarda zaman lafiya a sakatariyar. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Jam’iyyar ta APC dai tana fama da rikice-rikice a yan kwanakinnan tun bayanda kotu ta dakatar da Shugabanta na kasa Adams Oshimole.
Ko a jiyama Kungiyar gwamnonin jam’iyyar sun gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda suka tattauna muhimman abubuwa da zasu samar da zaman lafiya a jam’iyyar.