Yaushe Jam’iyyar APC Za Ta Fita Daga Rikice-Rikicen Cikin Gida?

0
203

Bisa dukkan alamu wutar rikici na ci gaba da ruruwa a jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, sakamakon dakatar da shugaban ta Adams Oshiomhole da kuma samun halartaccen wanda zai jagoranci jam’iyyar.

A ranar Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shirin halartar taron shugabannin gudanarwar jam’iyyar da bangaren Victor Giadom ya kira, wanda kuma ya halarta a yau, abin da ya batawa bangaren Bola Ahmed Tinubu rai, wadanda ke goyan bayan bangaren Prince Hilliard Eta dake cewa ba za su halarci taron ba. Bayan taron na yau, APC sun rushe kwamitin zartarwa na jam’iyyar, inda suka nada Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni a matsayin shugaban riko.

Wadansu bayanai na nuni da cewa; rahotanni sun ce Giadom na samun goyon bayan Gwamna Nasir El-Rufai da Kayode Fayemi da Simon Lalong da Abubakar Badaru da kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi, yayin da bangaren Tinubu ke da Gwamna Abdullahi Ganduje da wasu gwamnoni 17.

Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu y ace shugaban kasa ya goyi bayan Giadom ne saboda bin umurnin kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here