Za A Ɗaure Shugaban Hukumar Zabe Kan Ƙin Bin Umurnin Kotu

0
3964

Babbar kotun a jihar Neja wacce ke zama a Minna, ta baiwa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jihar (NSIEC), Aminu Baba Alhaji kwanaki 14 da ya tabbatar da ya bi hukuncin da ta yanke na baiwa dan takarar shugaban karamar hukumar Suleja Adamu Usaman takardar shaidar kasancewa zababben shugaban karamar hukumar Suleja dake jihar nasara bisa Abdullahi Shaibu na jam’iyyar APC. Umurnin da NSIEC har yanzu ba ta bi ba.

Kotun ta yanke hukuncin ne tun cikin watan Mayu inda wani mai suna Usman Idris ya karba a madadin shugaban hukumar zaben jihar a ranar 30 ga watan Mayun 2020.

Kotun ta tabbatar da dan takarar Jam’iyyar PDP Adamu Usman a matsayin zababben shugaban karamar hukumar ta Suleja tare da yin umurni ga hukumar zaben da ta karbe takardar shaidar nasarar zabe da ta baiwa dan takarar APC, Abdullahi Shu’aibu Maje ta baiwa Adamu Usman na jam’iyyar PDP.

Babbar kotun ta ce za ta daure shugaban hukumar zaben jihar mai zaman kanta idan wa’adin da ta ba shi ya kare ba tare da ya mika takardar tabbatar da cin zabe ga wanda ta baiwa nasara ba.

Idan ba a manta ba, Adamu Usman na jam’iyyar PDP ya yi nasara a karar da ya shigar a kotun sauraren korafin zabe na jihar Neja da kuma kotun daukaka kara a ranar 15 ga watan Yunin 2020,  bisa kalubalantar jam’iyyar APC wacce ta lashe zaben kananan hukumomi da a ka gudanar a watan Nuwamban shekarar 2019 da cewa sun shiga takara ba su da dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar wanda ya cika sharadin tsayawa takara. Sannan kuma an kara kalubalantar jam’iyyar ta APC da cewa sun shiga zabe alhali ba su da dan takarar kujerar mataimakin shugaban karamar hukumar.

A dalilin haka Adamu Usman da Jam’iyyar PDP ta nemi da kotun da ta tabbatar da Adamu Usman wanda ya zo na biyu a zaben a matsayin wanda ya yi nasara.  Inda kuma kotun ta tabbatar da wannan bukata, ta kuma bada umurni ga hukumar zabe ta jihar Neja da ta tabbatar da takardar nasarar  lashe zabe ga Adamu Usman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here