Za A Fara Zirga-Zirga Tsakanin Jihohi Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Janye Dokar

0
20094

Biyo bayan mika rahoton kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar Korona, a ranar Talata, gwamnatin tarayya ta amince da a fara zirga-zirga tsakanin jihohin kasar nan.

An kwashe  tsawon lokaci da hana shige da fice tsakanin jihohin Nijeriya saboda bullar cutar Korona. An sanya dokar ta yi aiki ne domin ya fara daga 4 na Asuba zuwa 10 na dare.

Shugaban kwamitin kuma Sakataren Gwamantin Tarayya, Boss Mustapha ya ce dama yana cikin aikin kwamitin bibiyar halin da ake ciki a kasar kan cutar korona tare da daukar sabbin matakai. Sannan har wala yau ya koka kan yadda mutane ke rikon sakainar kashi wajen daukar mataki duk da sun yarda akwai cutar.

Har wala yau gwamnatin ta amince dalibai ‘yan Firamare ‘yan Aji 6 da za su rubuta jarabawar su ta kammalawa, haka a matakin Sakandare ‘yan Aji 3 (JSS3) da 6 (SS3) wadanda su ma za su rubuta ta su jarabawar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here