Za a gudanar da sahihin zaɓe a jihar Ondo – Buhari

0
3382

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin ganin an gudanar da zaben Gwamnan Jihar Ondo cikin kwanciyar hankali wanda duniya zata amince da sakamakon sa.

Mai magana da yawun shugaban Femi Adeshina yace Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga magoya bayan Jam’iyyar sa ta APC a jawabin da yayi musu ta bidiyo.

Buhari ya yiwa mazauna Jihar Ondo alkawarin samar da tsaron da ya dace domin basu damar zuwa kada kuri’a cikin kwanciyar hankali da kuma tababcin ganin an kidaya kuri’un an kuma bada sakamako kamar yadda doka ta tanada.

Shugaban wanda ya bukaci magoya bayan Jam’iyyar sa da su zabi Gwamna Oluwarotimi Akeredolu domin cigaba da ayyukan alherin da yake a Jihar, yace ya gamsu da ayyukan dan takaran na su, domin ya taka rawar gani duk da matsalolin kudaden da ya fuskanta.

Zaben na Ondo na zuwa ne a daidai lokacin da Jam’iyyar APC ta sha kashi a zaben Jihar Edo wanda babbar jam’iyyar adawa ta lashe wajen ganin Gwamna Godwin Obaseki ya samu wa’adi na biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here