Za a raba wa jihohin ƙasar nan 36 da Abuja naira milyan 100-100 domin yaƙi da Korona

0
3333

Ministan Lafiya, Osagie Ehinare ya bayyana cewa ma’aikatar sa za ta rabawa jihohin kasar nan 36 da Abuja tallafin naira miliyan 100-100 domin cigaba da ayuukan dakile yaduwar Korona a jihohin su.

Ehinare ya ce wannan kudi daga cikin kudin wani shirin Bankin duniya ne domin kasashen kasashen Afrika Ta Yamma, tallafin annobar Ebola.

Bayan haka shugaban kwamitin shugaban Kasa, kan dakile yaduwar Korona, ya bayyana cewa kasar Indiya ta baiwa Najeriya gudunmawar maganin Chloroquine domin kula da marasa lafiya.

A karshe ya yi kira ga mutane su ci gaba da bin dokokin Korona.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 543 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Laraba.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –180, FCT-86, Kaduna-56, Edo-47, Ondo-37, Kwara-35, Ogun-19, Rivers-19, Kano-17, Ebonyi-16, Enugu-16, Delta-7, Bayelsa-4 Bauchi-3 da Abia-1

Yanzu mutum 38,344 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 15,815 sun warke, 813 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 21,716 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ce ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 13,806 FCT – 3,297, Oyo – 2,219, Edo – 2,064, Delta – 1,444, Rivers – 1,565, Kano –1,447, Ogun – 1,203, Kaduna – 1,267, Katsina –713, Ondo – 1001 , Borno –603, Gombe – 558, Bauchi – 534, Ebonyi – 715, Filato – 762, Enugu – 721, Abia – 527, Imo – 454, Jigawa – 322, Kwara – 706, Bayelsa – 326, Nasarawa – 289, Osun – 359, Sokoto – 153, Niger – 166, Akwa Ibom – 176, Benue – 294, Adamawa – 115, Anambra – 132, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 64, Ekiti – 86, Taraba- 54, Kogi – 5, da Cross Rivers – 29.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here