Zamantakewar Aure ta na buƙatar cika wasu manyan sharuɗa kamar haka

0
540

DANGANTAKAR MIJI DA MATA A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI DA NAZARIN HALAYYAR ƊAN ADAM

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Babu Wani Ɗan Adam Da Ya Cika Ɗari Bisa Ɗari, Sannan Babu Wasu Iyali Da Za Su Rayu Babu Saɓani Da Kura-Kurai A Tsakaninsu, Sai Dai A Yaba Kykkyawar Dangantakar Soyayya Wacce Za Ta Samar Da Kwanciyar Hankali A Manta Da Saɓani A Gina Zuri’a Ta Gari,

Iyali su ne tubalin gina al’umma. Raunin iyali kan rusa al’umma. Addinin musulunci ya riga ya yi bayani kan dangantakar da ke tsakanin iyali. Tasirin al’adun turawa da su ka shigo cikinmu ta hanyar kutsawa kafofin sadarwa su ne su ke neman rusa mana tsarin da addininmu na Musulunci ya gina mu akai. Maƙiya addinin musulunci sun himmatu wajen ƙarfafa bambance-bambance da rashin shugabancin saduwa da sunan ƴanci.

Martabar iyali da soyayyar iyaye su ne tushen tasowar yara cikin aminci da ƙoshin lafiya da hankali da lafiyayyen tunani da kyawawan ɗabi’u da ƙarfin imani mai cike da taƙawa da tsoron Allah.

  1. Zamantakewar Aure ta na buƙatar cika wasu manyan sharuɗa kamar haka:

(1. Soyayya da tausayi a tsakanin ma’aurata
(2. Sha’awa da gamsar da juna, (saduwar aure).
(3. Aminci da zaman lafiya.
(4. Sa’ido da kulawa da zuri’ar da za a haifa.

Waɗannan abubuwa ginshiƙai, Alƙur’ani ya yi bayaninsu kamar haka:

“Mun halatta muku matayenku daga haƙarƙarinku su kasance ni’ima a gare ku, mun sanya tausayi da jinƙai a tsakaninku.” (Q 30: 21). Da kuma:

“Allah Shi ne wanda ya halicce ku daga rai guda ɗaya na Annabi Adam sannan ya halicci matarsa Nana Hauwa’u daga gare shi domin ya samu nutsuwa daga gare ta” (Q7:189). Da kuma:

“Allah ya halatta muku matayenku a matsayin mallakinku da ƴaƴa da jikoki kykkyawar kyauta ce gare ku, yanzu kwa riƙe allolin ƙarya ko musanta alfarmar Allah ?” (Q16: 72). Da kuma:

“Matayenku gonakinku ne, ku je ga gonakinku a kowane lokaci ta yadda duk ku ke so, (banda ta dubura) kafin ku sadu da su, ku roki Allah ya azurta ku da ƴaƴa nagari masu taƙawa da tsoron Allah. Ku ji tsoron Allah ku sani cewar za ku haɗu da shi ranar gobe ƙiyama, ku yi kykkyawan albishir ga waɗanda su ka yi imani”. (Q2:223).

Halayya da ɗabi’a da aikin kowane ɗan gida ta kan shafi duk sauran ƴan gidan. Aiki ne akan iyaye su tabbatar kowane ɗan gida ya ba da gudunmawar ɗorewar martabar wannan gida. Uba shi ne ya ke da girman haƙƙin kula da iyali sama da Uwa kamar yadda za mu karanta cikin waɗannan ayoyin Alqur’ani da hadisan Manzon Allah SAW.

“Maza masu ba da kariya ne da kulawa da mata. Mata masu taƙawa lallai su yi ɗa’a ga Allah su kuma yi biyayya ga mazajensu su kuma kiyaye da duk haƙƙoƙin mazajensu ko da ba sa nan. Su kiyayewa mazajensu farjinsu da muhallansu. Matan da su ka aikata ba daidai ba ku yi musu wa’azi a karon farko idan sun ƙi ku ƙaurace musu wajen saduwar aure, idan sun ƙi ku doke su a hankali, amma ku gujewa dukansu a fuska da wurare masu tsada a jikin ɗan adam. Idan sun tuba sun dawo to ku gafarta musu, Allah shi ne mafi girma da ɗaukaka” (Q4: 34).

A hadisi kuma, wanda Abdullahi Ibn Umar ya ruwaito, Manzon Allah SAW ya bayyana cewa “kowa mai kiwo ne kuma za a tambaye shi kan kiwon da aka ba shi. Shugaba mai kiwo ne za a tambaye shi kan amanar waɗanda ya ke shugabanta, mai gida mai kiwo ne za a tambaye shi kan kiwon iyalinsa da aka ɗora masa, matar gida mai kiwo ce za a tambaye ta kan kiwon kula da gidan mijinta da haƙƙoƙinsa da ke kanta, bawa mai kiwo ne za a tambaye shi kan kiwon dukiyar mai gidansa da aka ba shi. Ku kiyaye, dukkanninku masu kiwo ne, kowa zai amsa tambaya kan kiwon da aka ba shi”. (Bukhari).

Mu kiyaye da samar da zuri’a marar amfani da amfanarwa. Idan ya kasance uba ko uwa akwai mai ɗauke da matsalar taɓin hankali ko rashin kula, to za a iya samun zuri’a marar amfani. Zuri’a marar amfani ita ce zuri’ar da ke tattare da rigingimu da rashin ladabi da biyayya da munanan halaye. Yaro ɗaya marar tarbiyya a gida zai iya shafawa sauran ƴan gida gabaɗaya domin mafi yawan yara su kan koyi ɗabi’un da su ka tashi su ka gani ana yi a gidansu. A ƙoƙarin samar da ƴaƴa nagari da kykkyawar zuri’a akwai buƙatar mutum ya siffatun da waɗannan ɗabi’u kamar haka: Nagarta, Afuwa, ilimi, sanin nazariyyar halayya da ɗabi’o’in mata, haƙuri, jajircewa, juriya da kuma iya fahimtar matsalolin wani ko halin da wani ya ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here