Zanga-zanga da fito-na-fito da shugabanni ba sa kawo alkhairi – Dakta Bashir Aliyu Umar

0
458

Babban limamin masallacin Alfurqan da ke birnin Kano, Dakta Bashir Aliyu Umar, ya bayyana cewa zanga-zanga da fito-na-fito da shugabanni ba sa kawo alkhairi.

Dakta Bashir Aliyu Umar ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke gabatar da huɗubar juma’a a masallacin sa na alfur’ƙan da ke unguwar Nasarawa a cikin birnin Kano.

Huɗubar jum’ar mai taken “zanga-zanga da Flfito-na-fito da shugabanni baya kawo alkhairi”. Babban limamin ya ƙara da cewa muddin aka samu wata zanga- zanga ta tabbata to hakika masallatai ba za su rayu ba, haka ma kasuwanni.

“Masallatai ba za su rayu ba, ba za a iya bude kasuwanni ba, masu sana’a ba za su samu yin sana’arsu ba, idan wannan al’amari na zanga-zanga da fito na fito da shugabanni ya dore”

Dakta Bashir Aliyu ya ƙara da cewa yayin da ake kira ga al’umma da su yi biyayya ga jagorori, to su kuma shugabanni yana da kyau su tsaya su ga sun sauke amanar da aka dora musu.

“Maslahar aminci da kwanciyar hankali shi ya fi akan a kawar da masu mulki da fitintinun zanga-zanga” in ji Dakta Bashir Aliyu Umar

“Shugaba inuwar Allah ne a bayan kasa, mu yawaita addu’a sannan mu dauki matakai, babba a cikin matakan shi ne mu koma ga Allah SWT sannan mu yi bakin kokarinmu wajen gyara kuskure a tsakaninmu” in ji Dakta Bashir

Haka kuma Limamin ya ce Idan fitina ta barke, masu mulki da masu jan ragamar al’umma ba za su iya, ana yawaitawa shugabanni addu’a domin idan suka mike abubuwan al’umma za su gyaru kuma za a samu nutsuwa.

Huɗubar juma’ar dai na zuwa ne a lokacin da al’ummar ƙasar nan su ka shafe mako biyu su na zanga-zanga a fili da kuma shafukan zumunta, suna zargin rundunar ƴan sanda da ke yaƙi da fashi da makami ta Sars, da cin zarafi da cin hanci da azabtar da mutane, ta hanyar amfani da maudu’ai daban-daban irinsu #EndSars.

A ƙarshen huɗubar babban limamin ya bayyana cewa ba sa tare da dukkanin wani zalunci ko azzalumin shugaba a ko ina ya ke.

“Muna barranta ga Allah da abubuwan da suke yi na zalunci ba ma tare dasu, amma muna tare da su a abubuwansu na daidai. Kuma muna musu addu’a Allah ya shirye su ya yi riko da hannunsu”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here