Zargin Sace Kuɗaɗe: Magu ya kwana a hanun hukuma

0
3299

Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu, ya kwana a hanun hukumar ‘yan sandan ciki bayan kamashi da aka yi a ranar Litinin.

Majiya mai tushe ta shidawa Majiyar Manuniya ta jaridar Daily Nigerian cewa, bayan hukumar DSS ta kama Magu, ta wuce da shi fadar shugaban kasa domin fuskantar Kwamitin bincike akansa, daga bisani aka wuce da shi sashen bincike na CID.

A ranar Litinin ne dai hukumar ‘yan sandan farin kaya suka kama Ibrahim Magu jim kadan bayan ya bar Ofishinsa dake Unguwar Wuse 2 Abuja bisa zarginsa da karkatar da kudaden da ake kwatowa daga barayin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here